Hukumar kula da dakile cututtuka ta Koriya ta fada ranar Lahadi 13 ga watan Disamba cewa Koriya ta kudu ta samu adadin masu kamuwa da cutar da ba a gani ba a baya cikin kwanaki 2 a jere na mutun 1,030.
A halin da ake ciki, Amurka ta bada amincewar gaggawa akan yin amfani da riga kafin cutar coronavirus, kuma riga kafin zai fara isa jihohin kasar gobe Litinin da safe, a cewar jami’ai. Wannan wani gagarumin ci gaba ne da aka samu a kasar da COVID-19 ta kashe sama da mutane 295,000, a cewar cibiyar samar da bayanan COVID-19 ta jami’ar Johns Hopkins.
Shugaban gudanarwar na shirin Warp Speed, wani shiri na samar da riga kafin cutar na gwamnatin Trump, Janar Gustave Perna, ya fada a wani taron manema labarai a jiya Asabar cewa kamfanonin jigilar kayayyaki zasu fara rarraba kimanin allurar riga kafin da kamfanin Pfizer ya hada guda miliyan 3 zuwa kusan cibiyoyin rabo 150, kuma karin wasu cibiyoyin kimanin 450 zasu sami riga kafin zuwa ranar Laraba.
A yammacin ranar Juma’a ne hukumar kula da abinci da magunguna ta Amurka ta FDA ta amince da riga kafin na kamfanin Pfizer, wanda ya hada tare da na BioNTech don amfanin gaggawa.