Kasashe G7 Sun Ci Alwashin Bunkasa Tattalin Arzikin Duniya

G7 Summit

Ministocin tattalin arzikin kasashe bakwai da suka fi karfin tattalin arziki a duniya, a yau Talata sun ci alwashin bunkasa tattalin arzikin duniya dake nuna alamun samun rauni sakamakon barkewar cutar coronavirus da ya shafi kasashe 70 da dokokin da zasu tallafa musu.

A wata sanarwa da suka fitar bayan wata ganawa da suka yi ta wayar tarho, ministocin sun ce, sun sa ido sosai akan yadda wannan al’amarin ya taba kasuwar duniya da kuma irin raunin da yake yiwa tattalin arzikin duniya, kuma zasu yi amfani da duk dokokin da suka dace domin bunkasa tattalin arzikin na duniya.

Sai dai ministocin basu bayyana takamamman matakan da zasu dauka na shawo kan cutar ba, a daidai lokacin da ake zuba masu ido su dauki mataki.

Tattaunawar da kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a duniya wato G-7, suka yi, na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jea-In, yake kokarin neman tallafin kudi da zai karo kayayyakin asibiti da kuma tallafawa kananan ‘yan kasuwa da suke jin jiki sakamakon rashin fitowar mutane da aka tilastawa zama a gida.

A halin da ake ciki kuma, yayin da adadin mutanen da suka kamu da cutar Coronavirus da wadanda cutar ta kashe ya karu a Amurka, shugaba Donald Trump ya ce, babu bukatar a ayyana dokar ta-baci a kasar a halin yanzu.

Sai dai shugaba Trump din ya ce, nan gaba idan bukatar hakan ta taso, zai iya ayyana dokar ta bacin a game da cutar ta Coronavirus.

Kawo yanzu mutane shida ne suka mutu a Amurka sakamakon cutar ta Coronavirus, dukkansu a arewa maso yammacin jihar Washington, inda jami’ai suka ce cutar ta shafe makonni shida ta na yawo ba tare da an sani ba.