Hukumar dalike cututtuka masu yaduwa a a Najeriya ta NCDC ta tabbatar da cewa mutane uku ke dauke da nau'in omicron a kasar yanzu haka.
Ranar Laraba 1 ga watan Disamba hukumar ta NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutun daya daga matafiyan biyu da suka shigo Najeriya daga Afirka ta Kudu a makon da ya gabata, wadanda tuni gwaji ya tabbatar su na dauke da sabon nau'in cutar da ke da saurin yaduwa.
Shugaban hukumar NCDC Dr. Ifedayo Adetifa ya fadi cewa, “ba abin mamaki bane idan aka samu wasu karin mutane da suka kamu da wannan cuta yayin da muke tattara sakamokon bincikenmu, kuma haka abin yake a ko ina a fadin duniya. A duk sa’a daya adadin na karuwa a kasashen da rahotantani suka ce an samu bulluwar cutar amma dai muhimmin abu shine muna kara sa ido kan lamura musamman ma akan matafiya da abubuwan da ake shigowa da su cikin kasar da kuma tabbatar da an bi matakan kariya.”
Darakta mai kula da tsare-tsare a hukumar lafiya a matakin farko ta Najeriya Dr Abdullahi Bulama Garba, ya ce su na kokarin tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun yi riga kafin cutar kuma dole ne bakin da ke shigowa Najeriya daga sauran kasashe sun nuna shaidar ba sa dauke da cutar coronavirus.
Duk da matakan tursasa jama’a da gwamnati ta dauka, har yanzu akwai wadanda suka kafe kan cewa ba za su yi riga kafin cutar ba yayin da wasu ke yi ba don son ran su ba.
Kwararren likitan kare lafiyar al’uma Dr. Adamu Danladi Daud, ya bayyana muhimancin karbar allurar mussaman a wannan lokaci da za a shiga yanayin hunturu. Ya na mai cewa abin lura shine ‘yan Najeriya da yawa basu karbi riga kafin ba, wannan babban hadari ne sosai don yawan wadanda suka yi riga kafin bai isa ya sa jama’a su kare juna ba.
A jiya Laraba ne dai dokar hana ma’aikatan gwamnati da ba su yi riga kafi ba a Najeriya shiga ofis ta fara aiki, kuma tuni hukumar NCDC ta shawarci ‘yan kasar da su yi amfani da damar da ake da ita yanzu don yin riga kafin cutar COVID-19 don kare kansu.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim.
Your browser doesn’t support HTML5