Kasashe 10 Sun Samu Gurbi A Gasar Cin Kofin Duniya

A sakamakon wasanni da aka gwabza a wasu sassa na neman gurbin shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na shekara 2018, da za'ayi a kasar Rasha, ya nuna ciwar kasashe goma ne a yanzu haka suka samu gurbin shiga gasar.

Kasashen sune Brazil, Germany, England, Belgium, Iran, da Japan, sauran sun hada da Mexico, Saudi Arabia, South Korea da kuma mai masaukin baki kasar Rasha.

Bisa doka da tsarin hukumar kula da kwallon kafa ta Duniya (FIFA) kasashe talatin da biyu ne suke fafatawa a gasar ta cin kofin duniya daga nahiyoyi daban daban.

Yanzu dai a jiran kasashe ashirin da biyu ne wanda zasu cika lisafin kasashe 32, inda a yau za'a gwabza a nahiyoyi daban daban ciki harda nahiyar kasashen Afirka inda Mali zata kece reni da Ivory Coast.

Your browser doesn’t support HTML5

Kasashe 10 Sun Samu Gurbi A Gasar Cin Kofin Duniya - 3'11"