Bayan ziyartar wadanda suke jinya a wani asibitin Ankara, Firai ministan Turkiya Ahmet Davu-toglu yace, akwai kwakkwarar hujjar cewa, kungiyar ‘yan ta’adda mai ra’ayin aware-yana ambaton haramtacciyar jam’iyar Kurdistan Workers da ake kira PKK, ce ke da alhakin harin.
Yace duk lokacin da kungiyar ta fuskanci matsin lamba da takurawa, sai ta kai irin wadannan hare haren kan farin kaya domin jefa al’umma cikin rudani.
Dovutoglu yace, jami’ai sun kama mutane goma sha daya da ake kyautata zaton suna da hannu a harin bom din, sai dai bai ambaci sunan macen da suka ce tana daya daga cikin maharan biyu ba. Yace, an haifeta a shekarar alib da dari tara da casa’in da biyu, kuma tayi zama a birnin Kars dake gabashin Turkiya, ta kuma shiga kungiyar PKK a shekara ta dubu biyu da goma sha uku. Kawo yanzu ba a bayyana maharin namiji ba.