Matakin bude iyakar da Togo ta yi ya biyo bayan hari mai nasaba da ta'addanci da aka ce wasu 'yan bindiga masu halaka da kungiyar al qaeda sun kai a kasar da ya yi sanadiyar mutuwar sojojin kasar su takwas tare da jikkatar wasu.
Mataimakin kwamishinan hukumar shige da fice a kan iyakar Ghana da Togo Aflao da Lome Duodu Fredrick ya fadawa manema labaru cewa, duk da bude iyakar za su karfafa tantace matafiya masu shige da fice.
A hirar shi da Muryar Amurka, Mallam Irbad Ibrahim mai sharhi kan harkakokin tsaro yace bude iyakar ita ce mafi katari musamman ga masu hada hadar kasuwanci duk da fargabar wasu aluman Ghana ke ciki sabida harin Togo.
Shi kuwa darektan cibiyar da ke baiwa kasashen yammacin Afrika shawara bisa tsare tsarensu masu nasaba da tsaro West Africa Centre for Counter Extremism, Muntari Mumuni yace bude iyaka shakka babu zai bunkasa harkar kasuwanci amma binciken baya bayan nan ya nuna cewa, 'yan ta'adda na daf da kawo hari a Ghana don haka sai ayi la'akkari sosai.
Tuni gwamnatin kasar Ghana ta gargadi addinai da su dauki matakin makala kamarori tare da samar da 'yan gadi a guraren taruwarsu domin dakile yunkurin hare hare.
Kasashen da suka kewaye Ghana wato Cote Dioire da Burkina Faso da Togo duk sun fuskanci harin ta'addanci.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5