Kasar Syria ko Sham ta dada yin kusa da yiwuwar fuskantar takunkumin kungiyar kasashen Larabawa, a sa’ilinda yawan wadanda ke mutuwa a tashe-tashen hankula na adawa da gwamnati ke karuwa.
Wa’adin da kungiyar kasashen Larabawa ta bayar ga Syria ta amince da masu sa ido na kasa da kasa, ko kuma ta gamu da karin hukunci, ya wuce ba tare da kasar ta Sham ta ce uffan ba. To amman ministocin kungiyar sun ce sun bai wa Sham har zuwa karshen jiya Jumma’a ta bayyana matsayinta.
Sakatare Janar na kungiyar ta kasashen Larabawa Nabil el-Araby y ace ya sami wasika daga kasar ta Sham da ke kunshe da tambayoyi game da batun masu sa ido din.
Kungiyar ta dakatar da Syria makonni biyu da su ka gabata saboda amfani da karfin tsiya wajen kokarin murkushe ‘yan adawa da kuma gazawar Shugaba Bashar al-Assad wajen aiwatar da shawarwarin da kungiyar ta bayar don kawo karshen tashin hankalin.
Wakilan kungiyar za su sake ganawa a yau Asabar don tattauna yiwuwar kakaba wa Sham takunkumi.
Kungiyar Sa Ido Kan Al’amuran Hakkin Dan Adam a Syria ta gaya wa Muryar Amurka cewa jami’an tsaro sun hallaka akalla mutane 8 a fadin kasar.
A halin da ake ciki kuma, jiya Jumma’a sojojin Sham sun bayyana cewa wasu ‘yan ta’adda sun kashe wasu matukan jiragen samansu 6 da wasu ofisoshin soji su 3. Kamfanin dillancin rabaran gwamati, SANA a takaice, y ace al’amarin ya auku ne a yankin Homs a ranar Alhamis.
Tashe-tashen hankula sun barke a jiya Jumma’a sa’ilinda masu zanga-zanga su ka basu bisa tituna a birane masu yawa, su na bukatar Mr. Assad ya yi murabus. A wani gefen kuma, kafafen yada labaran gwamnati sun bayar da rahotanni cewa magoya bayan gwamnati su ma sun yi gangami sun a ta kada tutocin kasar ta Sham da kuma hotunan Shugaban kasar don bayyana rashin amincewarsu da shawarwarin kungiyar kasashen Larabawa.