A yayin da 'yan Najeriya ke bukukuwan samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka, wasu kuwa 'yan Najeriya da suka fice zuwa kasar Libiya ne dai aka dawo dasu kasar, a ranar bukin samun 'yancin kai, bayan da suka makale a
kasar ta Libiya.
Hukumar bada agaji ta kasa ta karbi bakoncin wasu 'yan Najeriya 161, da aka dawo dasu daga kasar Libiya, Alhaji Idris Muhammad, babban jami'in hukumar me kula da shiyyar Legas, yayi wa wakilin muryar Amurka Babangida Jibrin, karin haske game da lamarin 'yan gudun hijiran da aka karba a babban filin jirgin saman kasa-da-kasa na Murtala Muhammad dake Legas.
Babban Jami'in ya kara bayani akan yadda wadansu daga cikin mutanen basu da takardu, wasu kuma an kama su, sun dade suna rufe a gidan kurkuku a Libiya, domin haka, dawo dasu gida shine yafi masu alheri, da kwanciyar hankali.
Muna dauke da rahoto cikin sauti da wakilin mu Babangida Jibrin ya hada muna.
Your browser doesn’t support HTML5