Kasar Kenya ta fara fuskantar sake barkewar coronavirus, bayan makwanni uku da ta dage wasu muhimman dokokin dakile yaduwar cutar.
Ministan kiwon lafiyar Kenya yayi kashedi a ranar Lahadi cewa kasar na cikin mawuyacin hali bayan da aka sanar da samun sababbin kamuwa 600 da mace mace da dama.
Wakilin Muryar Amurka a Nairobi yace masana sun ce akwai yiwuwar fuskantar kalubale idan aka sake kakaba dokokin hana zirga zirga.
Jami’an kiwon lafiya sun fargar da jama’a bayan da kasar ta samu sababbin kamuwa da cutar a cikin ‘yan makwanni da aka sassauta dokokin takaita yaduwar cutar.
Ministan kiwon lafiya Mutahi Kagwe yace mutum bakwai suka mutu da cutar a ranar Lahadi kana wasu 685 suka kamu da cutar a cikin kasar.