Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dage Dokar Hana Fita a Kenya


Shugaba Uhuru Kenyatta
Shugaba Uhuru Kenyatta

Dage dokar hana fiche da shige a gundumomin Monbasa da Mandera da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bada umurni ya fara aiki yau talata.

Kenyata ya ce kada mutane su dau sassauta dokar tafiye tafiya da wasa, su guji yin sakaci.

Kenyatta ya kuma sanar da fara sufurin jiragen sama tsakanin kasa da kasa ranar 1 ga watan Agusta yayin da sannu a hankali suke bude kasar.

Shugaban na Kenya ya sake tsawaita dokar hana zirga zirga a kasar baki daya daga karfe 9 na dare zuwa karfe 4 na asuba na wasu kwana 30 nan gaba. Yana mai gargadin cewa, idan al’ammura suka dada rincabewa Kenya zata sake kulle kasar.

Kasar ta Kenya ta samu mutum sama da dubu 8,000 wadan da suka kamu da cutar coronavirus yayinda 164 suka mutu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG