Kasar Iraqi Zata Yi Musayar Bayanan Siri da Wasu Kasashe Akan Yaki da ISIS

Mayakan ISIS

Kasar Iraqi zata yi musayar bayanan siri da kasashen Rasha da Iran da Rasha akan yaki da ISIS

Kasar Iraqi tace zata yi musayar bayanan sirin tsaro da Syria, Iran da kuma Rasha don yakar ‘yan kungiyar ISIS. Kakakin Firaministan Haider Al-Abadi yace, gayyar masana tsaron za su lura da zirga-zirgar ‘yan ISIS da kuma dakile karfinsu.

Ba dai wani bayanin kulla wata ‘yarjejeniya, amma a bayyane yake irin yadda kasar Rasha ke kara tasiri a yankin. Rasha dai ta jibge jirage da wasu karikitan yaki a sansanin sojan samanta a Syria.

Jami’an sojan Amurka sun ce ga alama Rasha na kare kadarorinta ne da ke Syria. Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace har yanzu ba'a san manufar Rasha ba.

Kakakin rundunar mayakan da Amurka ke jagoranta na yaki da ISIS Kanar Steve Warren yace, Amurka ta kalubalanci kasancewar Syria cikin kasashen da zasu sami bayanan sirri ba. Yace, basu amince da shigar Syria cikin musayar bayanan ba.

Musamman idan aka yi la’akari da yadda ita da kanta Syria din ke nuna rashin imani wajen hallaka al’ummarta da kanta. Mista Kerry kuma ya fada a birnin New York cewa, yaki da ISIS dole sai an shirya. Kerry na ganin wannan sabon kawacen da Rasha bai shirya ba.