Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Nemi A Gudanarda Cikakken Bincike Kan Mutuwar Mahajjata 717


Shugaban Iran Hassan Rouhani.
Shugaban Iran Hassan Rouhani.

Iran ce ahalin yanzu tafi hasarar 'yan kasarta a bala'in da ya auku.

Iran kasar da ahalin yanzu tafi ko wacce yawan hasarar mahajjata sakamkon turereniyar data auku na Minna har mutane 717 suka halaka kusa da Makka,ta bukaci hukumomin Saudiyya su gudanar da cikakken bincike da kuma neman ganin an tallafawa sauran mahajjatanta wadnada wanan iftila'in ya rutsa dasu.

An gudanar zanga zanga a duk fadin Iran jiya jumma'a, inda masu zanga zanga suke Allah wadai da kasar Saudiyya saboda yadda ta dauki wannan hadari data auku ranar Sallar layya.

Banda yawan mutane da suka rasu fiye da mutane 900 sun sami raunuka. Hukumomi a Farisan sun ce akalla 'yan kasar 131 ne suka mutu a Mina,wasu 'yan kasar 85 suna daga cikin wadanda suka jikkata, wasu kuma har yanzu ba'a san inda suke ba.

Kafofin yada labarai a Morocco sun ce 'yan kasar 87 ne suka halaka, haka nan wasu kasashe Afirka masu yawa ciki har da Najeriya sun bayyana cewa 'yayan kasashen suna daga cikin wadnada suka halaka. Sauran kasashe da musibar ta shafa sun hada da India, da Indonesia, da Pakistan da kuma Netherlands.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ahalin yanzu yake nan Amurka domin taron babban zaure na MDD yace wannan hasara ba ga iyalai da kasashen wannan musiba tashafa kadai ba amma ga illahirin al'umar musulmi.

XS
SM
MD
LG