Kasar India ta sanar da cewa tana shirye shiryen harba wani jirginta zuwa duniyar wata.
Shugabana hukumar kula da sararin samaniyar India, K Sivan, ya fadawa manema labarai a ranar Alhamis cewa, India ta ware shekarar 2030 a matsayin shekarar da za ta aika jirgin sararin samaniyar mai nauyin tan 20.
Ya kuma kara da cewa India ba zata hada kai da ko wace kasa ba a wannan gagarumin aiki da zata yi.
Sivan ya ce jirgin mai yawo a samaniya za su yi amfani da shi ne wajen taimakawa wani jirgin India na farko da za ta tura mutum zuwa sararin samaniya.
Hukumar kula da sararin samaniyar ta fara shirye shirye don ta tura' yan sama jannati uku zuwa sararin samaniya a shekarar 2022.
Aikin na sararin samaniyar wani babban ci gaba ne ga India don ta cimma burinta na yin bincike a sararin samaniyar.