Kasar Ghana Tana Shawarar Dawo Da 'yan Kasarta Dake China Gida

Coronavirus

Tuni Wasu Kasashe Suka Fara Kwashe 'Yan Kasar Su Daga Birnin Wuhan Dake China Kuma Tushen Cutar CORONAVIRUS Wacce Humkumar Lafiya Ta Duniya WHO Ta Ayyana Dokar Ta Baci Akanta.

Yayin da hukumomin kasashen duniya ke kokarin kare al’ummominsu dake kasar china daga kamuwa daga cutar coronavirus wace majalisar dinkin duniya ta bayyana ta a matsayin annoba, itama kasar Ghana ta shiga sahun kasashen dake tunanin daukan wannan mataki.

Duk da cewa wannan lamarin na bukatar kulawa na gaggawa, ba a iya aiwatar da wannan aiki cikin sauki ba tare da kashe makudan kudade ba wanda a halin yanzu kasar ta Ghana, bata da irin wannan kudi a ajiye.

Ofishin jakadancin Ghanan, ya ce, zasu fi mai da hankali ne akan maido dalibai da ‘yan kasuwa daga China daga cikin kudade kalilan da gwanati ta bayar, wanda jami’an ofishin jakadancin suka ce, yanayi ne mawuyaci amma ya zama dole su dau matsaya.

A saurari Cikakken Rahoton Ridwan Abbas:

Your browser doesn’t support HTML5

Kasar Ghana Na shirin kwashe 'yan Kasar dake China