Kasar Chile Ta Zamanto Zakaran Gasar Copa America A Karo Na Farko

Chile's goalkeeper Claudio Bravo lifts the Copa America trophy after defeating Argentina in the final soccer match at the National Stadium in Santiago, Chile, Saturday, July 4, 2015. Chile became Copa America champions for the first time after defeating A

Kasar Chile ta zamanto zakaran wasan Copa America a karo na farko a tarishin kasar, bayan da ta sami nasarar doke kasar Argentina 4-1 alokacin buga kwallon daga kai sai Gola.

‘Yan wasan Argentina Gonzalo Higuain da Ever Banega sun sami rashin sa’ar shigar da kwallo raga alokacin da suke buga da kai sai Gola, a daya bangaren kuma Alexis Sanchez da sauran ‘yan wasan Chile sun kawo karshen katutun rashin sa’ar kusan shekaru ‘dari.

An kare wasan na mintuna 90 ba tare da saka kwallo ko daya a raga ba, haka zalika bayan an kara lokacin wasan duk da yake masu bakuncin wasan sun mamaye kasar ta Argentina.

Kafin wasan na jiya Asabar kasar Chile sau daya kacal ta taba samun nasar kan kasar Argentina a wasanni 38 da suka buga a baya.

Wannan dai shine wasan karshe na biyu da Lionel Messi da sauran tawagarsa suka sami rashin nasara a wannan shekarar, idan aka tuna da kwallon da Mario Gotze ya zarga a raga lokacin wasan karshe na gasar cin kofin duniya, wanda yasa kasar Germany ta lashe wasan.