Karshenta Dai Lionel Messi da FC Barcelona ne Suka ci Kasuwarsu - 23/03/2014

Lionel Messi na FC Barcelona, wanda ya jefa kwallaye 3 a ragar Real Madrid, lahadi 23 Maris 2014

Lionel Messi ya jefa kwallaye har uku yayin da FC Barcelona ta je har gida ta lashe Real Madrid da ci 4-3.

Kwallaye uku da Lionel Messi ya jefa, ck=ikinsu har da biyu daga bugun fenariti, sun ingiza FC Barcelona ta doke Real Madrid a wasan karon batta da kungiyoyin biyu suka buga yau lahadi a filin wasa na 'yan Real, watau Santiago Bernabeu.

Messi, wanda shi ne dan wasan Barcelona dea ya fi jefa ma kulob din kwallaye a raga a tarihinta, ya jefa buguna fenariti har biyu a bayan da aka komo daga hutun rabin lokaci, na biyun a bayan da Xabi Alonso ya kayarda dan wasan Barcelona mai suna Andres Iniesta.

Da wannan nasara, yanzu ratar maki 1 kawai Real Madrid (da abokiyar adawarta ta cikin birnin Madrid, Atletico Madrid) suka ba Barcelona a saman teburin wasannin lig-lig na kasar Spain.

Iniesta na Barcelona shi ya fara jefa kwallo a raga, amma dan wasan Real Madrid, Karim Benzema, ya jefa kwallaye biyu ya dira kungiyarsa a gaba. Messi ya jefa ma Barcelona kwallo na biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci, amma Cristiano Ronaldo ya sake maida Real gaba a wani bugun fenariti.

Kafin wannan wasa, an yi ta hasashen cewa Ronaldo da Gareth bale da Neymar da kuma Messi sune zasu mamaye wannan karawar kungiyoyin biyu da ake lakabawa suna El Clasico a duk lokacin da suka buga, amma sai sauran ukun suka kasa tabuka wani abu, aka bar Messi kawai ya ci kasuwarsa a babban birnin na Spain.