WASHINGTON, DC —
Chelsea da Liverpool sun jefa kwallaye shida-shida a ragar abokan karawarsu, ita ma Manchester City ta zura guda biyar.
Arsene Wenger, manajan Arsenal ya dauki cikakken alhakin dan karen dukar da kungiyarsa ta sha yau asabar a hannun Chelsea da ci 6-0, a ranar da kungiyarsa ta buga wasanta na dubu 1 karkashin jagorancinsa.
Manajan na Arsenal ya bayyana wannan kashi da Gunners suka sha a zaman ranaku mafiya muni tun lokacin da ya fara koyar da wasan kwallon kafa.
Yau dai rana ce ta ruwan kwallaye a gasar firimiya ta Ingila, domin ita ma Manchester City, ta doke Fulham da ci 5-0. Liverpool ta lallasaa Cardiff City da ci 6-3.