Karin Magana Mai Kwatantawa

Dr. Abdullahi Garba Imam

A cikin shirin mu na Karin Magana haryanzu muna tare ne da Dakta Abdullahi Garba Imam wanda a yau yayi mana bayani kan Karin Magana mai kwatantawa.

Karin magana mai kwatantawa shine wadda ta kunshi wasu kalmomi na musamman da ake amfani da su, missali ana amfani da wadannan kalmomi da suka hada da “kamar, saikace, kai kace, tamfar,” da dai sauransu.

Babban malami Mohammad Sa’idu Gusau, na cewa a kwatanta abu biyu masu hali daban daban ta amfani da wasu kalmomi missali irin su “ace, kamar, sai kace, kai kace, tamkar da sauransu” missalan ire iren wadannan karin magana kuwa sune kamar ace “na saki raina kamar tsumma a randa” to idan aka duba za’a ga cewa tsumma a randa na kwanciya ne, to shima mutum idan hankalinsa ya kwanta ya samu nutsuwa za’a ga hankalinsa ya kwanta.

Sai kuma karin magana ta gaba wadda ake cewa “kana kau da kai ya kadangaren gobara” wannan na nunin yadda za’a ga kadangare daga cikin toka baki kirin da shi ya hau kan garu yana kada kai, to mutane na cewa alokacin da yake kada kansa yana cewa Allah ya kiyaye da dani za’a kone.

Domin sauraren cikkaken bayanin Dakta a danna nan a saurara.