Kungiyar Kwadago ta NLC a Najeriya ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su "gaggauta" janye karin farashin litar mai da aka yi kasar.
A ranar Laraba Kamfanin man kasar na NNPCL ya kara farashin man zuwa 1,030 daga Naira 898.
Wannan shi ne kari na biyu cikin kasa da wata guda da kamfanin ya yi lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce.
“Muna masu takaici da karin farashin man fetur na baya-bayan nan. Kamar yadda muka gani, wannan gwamnati ba ta da wani abu da aka fi saninta da shi sai dai karin farashin man fetur ba tare da la'akari da karfin daukar nauyin 'yan Najeriya ko samar da wani matakin sassauci ba.
“Abin takaici ne a ce wani kamfani mai zaman kansa (NNPCL) ne yake kayyade farashi.” Wata sanarwa da Shugaban NLC Joe A jaero ya fitar a ranar Laraba ta ce.
“Muna kalubalantar gwamnati da ta koma kan teburin tsare-tsare don ta gabatar mana da wani tsari na ci gaban tattalin arziki da hadin kai da ci gaban kasa, maimakon wannan yanayin tsalle-tsalle na tsare-tsare na wucin gadi da matakai na taimakon gaggawa.” Ya kara da cewa.
A cewar NLC wannan karin na baya-bayan nan ya sake sauya lissafin rayuwar 'yan Najeriya a lokacin da suka kokarin neman mafita kan halin da suke ciki.
“Wannan karin zai kara zurfafa talauci yayin da karfin masana'antu zai ragu, ana rasa ayyuka sakamakon wannan mataki.
“A bisa wannan dalili, muna kira ga gwamnati da ta gaggauta janye wannan karin farashin tun da karin da aka yi a baya bai haifar da wani sakamako mai kyau ba. Mutane sai kara talaucewa suke yi.” In ji shugaban na NLC.
Sai dai kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa farashin danyen mai a kasuwannin duniya ne ke yin musababbin karin farashin litar mai a kasar.
Kamfanin ya bayyana hakan ne ta bakin babban daraktan sashen kasuwanci da cinikayyarsa, Alhaji Lawal Sade.
A cewar kamfanin, zai tabbatar da cewa ana samun wadataccen mai a fadin kasar.
Saurari cikakkiyar hirar wakiliyar Sashen Hausa na Muryar Amurka, Halima AbdulRa'uf da Alhaji Sade:
Your browser doesn’t support HTML5