Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DSS Ta Saki Shugaban NLC Joe Ajaero


Shugaban NLC, Comrade Joe Ajaero, tsakiya sanye da bakar riga, bayan da ya dawo daga amsa gayyatar 'yan sanda makonni biyu da suka gabata (Hoto: Facebook/NLC)
Shugaban NLC, Comrade Joe Ajaero, tsakiya sanye da bakar riga, bayan da ya dawo daga amsa gayyatar 'yan sanda makonni biyu da suka gabata (Hoto: Facebook/NLC)

Rahotanni sun ce duk da an saki Ajaero, hukumar ta DSS ta kwace masa fasfo dinsa na tafiya.

Rahotanni daga Najeriya na cewa Hukumar ‘yan sandan farin kaya ta DSS ta saki shugaban kungiyar kwadago, Joe Ajaero bayan da ta kama shi a yinin Litinin.

An kama Ajaero ne a filin tashin jirage na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja yayin da yake hanyarsa ta zuwa wani taron kungiyoyin kwadago a Birtaniya.

Gidan talabijin na Channels ya ce Ajaero ya tabbatar da sakin nasa, inda ya bayyana cewa hukumar ta DSS ta bar shi ya tafi gida da misalign ƙarfe 11 na daren Litinin.

Kazalika jaridar Punch ta ruwaito tsohon dan takarar shugaban kasa kuma dan fafutuka kare tsarin dimokradiyya Omoyele Sowore yana cewa an ba da belin Ajaero.

Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya ya bayyana cewa an yi masa tambayoyi na tsawon sa’o’i 15 bayan an kama shi da misalin karfe 7 na safe.

Rahotanni sun ce duk da an saki Ajaero, hukumar ta DSS ta kwace masa fasfo dinsa na tafiya.

Bayanai sun yi nuni da cewa jami’an hukumar ta DSS sun masa tambayoyi kan zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a farkon watan Agusta.

Kama Ajaero na zuwa ne kasa da makonni biyu bayan da ‘yan sanda suka gayyace zuwa ofishinsu a Abuja kan zargin hannu a ayyukan ta’addanci da aikata manyan laifuka a yanar gizo.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG