Wanan kira da 'yan majalisar suka yi, ya biyo bayan wani korafi ne da 'yar majalisa daga jihar Ogun, Omowumi Oguntola ta kawo a zauren majalisar, inda ta ce a kwai karancin mata masu rike da mukaman siyasa a Najeriya.
Sannan kuma ta bada shawara cewa za a iya yin gyara idan shugaba Buhari ya nada karin mata a matsayin shuwagabannin ma'aikatu, tunda an riga an zana sunayen ministoci inda aka samu mata 7 kacal cikin ministoci 43.
Wanan ya janyo hankali Farfesa Grace Jokthan ta Budaddiyar Jami'a da ke Abuja, har ta nuna jin dadin ta cewa an samu karin mata a cikin ministocin, ta kuma bada shawara cewa su yi aiki domin su bada kunya, a ganin ta hakan zai sa a samu karin mata a gaba.
Amma tsohuwar Darekta a Cibiyar Bincike ta Kasa Ramatu Mustapha Bashir, ta ce lallai Buhari ya yi kokari, amma tana fata za a ba mace ministan kula da harkokin noma, saboda a yanzu mata sun shiga harkar noma gadan-gadan, kuma suna bukatar taimako. Ta kara cewa idan mace na shugabantar ma'aikatar, za ta taimaka masu sosai.
Onorabul Omowumi Oguntola, ta ca acikin 'yan majalisar dokokin Najeriya 469 mata 19 ne a ciki, 12 na majalisar wakilai, sannan 7 na majalisar Dattawa, wanda yake kashi 4.1 kenan a cikin 100. Kuma haka ya sha banban da yadda yake a wasu kasashen Duniya.
Medina Dauda ta hada muna wannan rahoton cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5