Babbar damuwa a fannin kiwon lafiya a Najeriya, kasa mafi yawan al'uma a nahiyar Afirka, ita ce rashin wadatattun ma’aikata kuma aiki ya yi karanci.
A cewar Dakta Christopher, dan kasar Uganda wanda ke da kamfanin samar da kiwon lafiya ga al’umomi, tamkar an manta da batunsu.
Jaridar Premium Times ta wallafa labarin da ke nuna yadda larabawa ke daukar likitoci daga Najeriya zuwa musammam ma Saudiyya.
Shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko na Gombe, Dakta Ahmad Gana, ya ce kalubalen ba na albashi ba ne kadai har ma da na karancin kayan aiki wanda kan sa kwararrun likitoci ficewa don samin manyan asibitoci da za su ba su damar nuna kwarewarsu.
A cewar Dakta Ahmad, akwai bukatar gwamnatoci da masu kudi su rika zuba hannun jari a fannin kiown lafiya wanda hakan ne zai taimaka wajen bunkasa fannin.
Zai yi wahala a shafe shekaru guda ba tare da barazanar yajin aiki daga likitocin Najeriya ba, kan neman karin albashi da gyara asibitoci.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5