Ministocin da ke cikin tawagar sun hada da Abdulrahman Dambazau na harkokin cikin gida, da A’isha Abubakar mai kula da lamurran saka jari da kasuwanci, da Suleman Adamu minstan albarkatun ruwa, da Bawa Buhari na ma’adanai da kuma Zainab Ahmed ministan tsare tsare da kasafin kudi.
An tattauna kan batutuwa daban daban ciki harda mika koke ga shugaban kasa kan harkokin bunkasa ilimin zamani da gina jami’ar ilimi a jahar Kano, yayin da ministan labaru Lai Muhammed ya bada amsar cewa zasu mika wannan batu ga gwamnati kuma dama wannan ne makasudin shirya taron.
Dalibai daga jami’ar Bayero dake jahar Kano sun bayyana ra’ayoyin su akan irin tallafin da gwamnatin Muhammadu Buhari tace zata yi masu, da aika sako ga shuagaban kasa na cewa a taimaka a gaggauta basu tallafin kudi Naira dubu Biyar da aka alkawarta wa matasa da masu karamin karfi.
Ministan tsare tsare Zainab Muhammed ta yi Karin bayanin cewa dubu biyar din da gwamnatin ta ce zata ba marasa karfi da gajiyayyu ne amma a cewar ta tunda sun tattauna akan hakan zasu isar da wannan koke ga shugaban kasa.
Daga Kano ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5