Shugabannin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Fc, sun karawa koc Ibrahim A. Musa, mukami a matsayin mukaddashin babban kocin kungiyar har zuwa lokacin da kungiyar ta nada sabon mai bada shawara.
A cewar wani jawabi da jami’in yada labaran kungiyar Rilwanu Idris Malikawa, ya rattabawa hanu jim kada bayan wani zaman gaggawa da suka yi, shugabanin kungiyar sun amince da nada Usman Abdullahi, a matsayin mukaddashin babban shugaban karamar kungiyar wato Junior Pillars FC, da kuma Friday Christopher a matsayin mataimakin shugaban babbar kungiyar.
Shugabanin sun kuma bayyana tsohon kocin karamar kungiyar Junior Pillars FC, Koc Ahmed Garba Yaro, a matsayin kocin karamar kungiyar ba tare da bata lokaci.
Malikawa ya bayyana cewa shugaban kungiyar Alhaji Tukur wanda shine ya jagoranci zaman, ya bukaci daukacin ‘ya’yan kungiyar da su hada kawunansu domin ciyar da kungiyar gaba.
Kwamitin ya bayyana karin girman a matsayin wata hanya ta karawa matasan koc koc din kwarin gwiwa domin kaiwa wani matsayi a nan gaba.
Yanzu haka kungiyar ta sa wasu ‘yan wasanta guda hudu, kasuwa, kuma tana kan tattaunawa da wasu ‘yan wasa daga kungiyar ABS, da LOBI, Elkanemi da sauransu domin maye gurbin su a cewar Malikawa.
Daga karshe ya bayyana cewa zaman ya kasance tamkar gargadi ne ga wasu daga cikin ‘yan wasan domin su kara azama, yayinda wasu kuma kungiyar zata fara biyan su rabin albashi bisa rashin tabuka abin kwarai.