Wasu da aka zanta dasu a Kano sun ce wani bala'i ne ya afka masu inda yanzu 'yan kasar Sin suka shiga sana'arsu.
Yadda suke rina kaya a Kano ita ce 'yan kasar Sin ko China suka sata suna zuwa kasarsu su yi kana su kawo kayan su cika kasuwar Kano dasu duk da cewa daga wurinsu mutanen Kano ke sayan kayan rinin. Marinan suna da yara da suke koyon aikin a karkashinsu. Malam Bashir Dauda Aliyu Dawakin Kudu shugaban kungiyar marina tufafi a Kano yace shi kadai yana da yara dari a karkashinsa kuma kimanin mutane dubu talatin ne suke dogaro akan sana'a.
Yakubu Lawal Ishaya sakataren kungiyar masu rina tufafi ya fayyace irin mutanen dake anfana da sana'arsu kana ya kira gwamnati tayi wani abu dangane da barazanar da 'yan kasar Sin ke yiwa sana'ar tasu. Ya kira gwamnati ta sa 'yan China su tsaya akan kayan da suke kawo masu kamar su shadda da kayan rini. Su daina shigo da kayan da suka riga suka rina a can kasarsu.
Alhaji Kabiru Yau Babba wani dan kasuwa a kantin Kwari dake sayar da shadda da aka rina yace, da yana sayar da shadda daga Kamaru, Chadi da Nijar har ya kan yi cinikin nera miliyan bakwai ko takwas rana daya amma yanzu da kyar ya yi cinikin nera dubu bakwai domin kayan Sin sun kore masu kasuwa. Yace shigowar China Kano bala'i ne garesu.
Masana harkokin shari'a sun ce kowace kasa mai hankali dole ne ta kare wasu sana'o'inta da masana'antunta domin kada 'yan kasashen waje su kashesu. Haka ma ya zama wajibi kasa ta takaita irin abubuwan da za'a iya shigowa dasu domin na cikin gida su rayu.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5