Yanzu haka dai wadanda wannan iftala’I ya afkawa a karshen mako na karbar magani a asibitin kwararru na Murtala dake tsakiyar Birnin Kano.
Duk da cewa, galibin mutanen da wannan waki’a ta fadawa na cikin mawuyacin hali, amma wasu daga cikin su na yin karfin hali, inda har-ma su kan yi magana da manema labarai inda suka ce garin kashe gobarar ne feshin man ya abka masu.
Yayin da gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin yin magani ga wadannan mutane, hukumomin kwana-kwana a jihar sun yi tsokaci game da musabbabin wannan gobara. Alhaji Hassan Ahmed Mohammed, shine Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kanon. Ya kuma ce rashin bin ka'idojin DPR ne ya ke janyo irin wadannan hatsarin.
Daga nan Alhaji Hassan Ahmed Mohammed ya shawarci masu gidan mai a jihar kan abin da ya kamata su yi da suka hada da tabbatar da cewa suna da kayan aikin kashe wuta a kowani lokaci kuma ana sabis dinsu akai-akai.
Saurari cikakken rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5