Kano: Hizba Ta Ce Za Ta Sa Kafar Wando Daya Da Wadanda Ke Tsangwamar Masu Abaya

Abaya

'Yan mata a jihar Kano da ma sauran jihohin arewacin Najeriya na fuskantar matsanaci tsangwama daga bangaren samari dangane da sanya abaya da ta shigo kwanan nan.

A baya bayan nan ne dai 'yan mata suka sha alwashin gudanar da wankan abaya a sallar karama da ta wuce, bisa rashin sanin cewar hakan zai zo da tangarda.

Idan za’a iya tunawa, a lokacin azumin watan Ramadan din da ya gabata, zuwa lokacin barbar sallar karama ne 'yan mata suka sha alwashin yin ankon abaya, wanda ya karade kafar kafafesada zumunta na cewa a bana ankon zasu yi.

Amma 'yan matan ba su san hakan zai musu cikas ba ga wannan kudirinasu.

A yanzu hakan dai mata na fuskantar barazana da zarar sun sanya abaya.

Wasu 'yan mata da Muryar Amurka ta zanta da su, sun bayyana mawuyacin hali da suke tsintar kansu na sanya abaya a yanzu.

Sun ce ba za su iya saka abaya a yanzu ba saboda kure su da ake yi, yayin da daya daga cikinsu ta yi mana bayani cewar wajen da suka tafi da kawarta, yara ne suka ture ta har sai da jami’an tsaro suka zo suka ceceta, sannan ta tsira.

A don haka ne ta ce ta kaurace sa abaya a yan kwanakin nan.

Abin da al’umma ke yi yanzu ga masu sanya abaya bai dace domin ba duk masu sanya abaya ne samarinsu suka saya musu abayar ba, wasu iyayensu ne suka saya musu a cewar wasu.

Ko me ya sa samarin ke tsangwamar yan matan kan sanya abaya?

“Laifin 'yan matan ne domin sun dauko abin da ba al’adar Bahaushe ba ne sannan ba abu ne mai dorewa kuma sun dauke abin kamar wani gagarurumin al’amari. Mafi yawan mata sun dorawa samari nauyin lallai sai ya yi wa budurwarsa abaya.

Shi ma wani da muka zanta da shi, cewa ya yi da zarar saurayi ya sayawa budurwarsa abaya, toh hakan na bada damar yin lalata da ita kenan. Hakan ce ta sa su ke kokari kawar da wannan sabon abu da ya shigo.

Dangane da hakan ne ma shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Harun Muhammad Sani Ibn Sina, ya yi tir da yadda al'umma ke tsamgwama ga masu sanya abaya.

Ya ce abaya shiga ce ta musulunci, sannan shari'a ba ta zo da wani kalar tufafi kwaya daya da za’a rinka sakawa ba, ta dai bayyana cewar a rufe dukkanin jiki ta hanyar rufe gabobi guda shida da musulunci ya gindaya.

Don haka ya ce abaya na daga cikin tufafin da ke rufe dukkanin suturar mace da aka umarce ta da ta rufe shi. Sannan kada a sanya kayan da ya yi kama da kayan irin ta maza.

A halin da ake ciki dai sanya abaya ya zama jidali ga mata, ko da yake, hukumomi a jihar ta Kano sun ce za s fara hukunta masu yin tsangwamar.

A halin da ake ciki, hukumomin a jami'ar kimiyya da ke Wudil, na neman wasu dalibai maza da suka nuna tsangwama ga wata daliba wacce ta sanya abaya, lamarin da ya karade shafukan sada zumunta.