KANO: Halin Da Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa a Kano Ke Ciki

Rabon kayan tallafin kayan agajin gaggawa a jihar Kano da ke Najeriya

Mutanen da ambaliyar ruwa ta lalata musu gonaki da gidaje a jihar Kano da ke Najeriya na ci gaba da korafi kan yadda hukumomin jihar da-ma na tarayya suka yi watsi da makomar su.

Wannan na faruwa ne duk kuwa da irin kuncin rayuwa da suke fuskanta saboda rushewar muhalli da karancin abinci. Sai dai hukumar bada agajin gaggawa ta jihar ta mayar da martani.

Wata kididdiga da hukumomin jihar ta Kano suka fita ta nuna ambaliyar ta bana ta rusa gidaje dubu 36, 254 a 34 daga cikin kananan hukumomin jihar 44.

Iftila’in ambaliyar ya lalata jimlar gonaki dubu 14, 364 a sassan jihar ta Kano yayin da aka rasa rayukan mutane 23 sai kuma wasu fiye da 100 da suka jikkata sanadiyyar wannan ambaliya.

Watanni biyu zuwa uku da daukewar ruwan sama a wasu sassan arewacin Najeriya, yanzu haka, hukumar bada agajin gaggwa ta jihar Kano ta ce ta fara rabon kayan tallafi ga wadanda ambaliyar ta shafa.

A zantawa da wakilin Muryar Amurka na Kano, Mahmud Ibrahim Kwari, Sakataren zartarwa na hukumar, Alhaji Sale Aliyu Jili, ya ce yanzu haka hukumar hadin gwiwa da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa suna aikin raba kayayyakin tallafi da suka hada da kayan abinci da na gine-gine wadanda kudin su ya kai Naira biliyan biyar.

Ambaliyar ruwa a jihar Kano da ke Najeriya

Bisa ga cewar shi, wannan bai hada da mutanen da ambaliyar ruwan ta lalata gonakin su ba. Yana mai cewa, tallafin gonaki na nan tafe bayan kwamitin shugaban kasa karkashin ministan ruwa ya kammala aikin sa.

Sai dai wasu daga cikin magidanta da wannan Iftila’i na ambaliya ya ritsa dasu a kananan hukumomi irin su Warawa, Wudil da Ajingi na kokawa kan yadda hukumomin biyu ke rabon kayan tallafin, suna masu cewa, ko da yake suna da labarin rabon tallafin, amma su bai kai gare su ba. Yayin da wasu daga cikin su ke cewa, hatta wadanda suka samu, abin da aka basu bai kai ya kawo ba.

To amma sakataren zartarwa na hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano Alhaji Sale Aliyu Jili ya ce wadanda ke korafin ba sa cikin jerin mutanen da jami’an sa suka tantance lokacin da lamarin ya faru, don haka ba sa cikin wadanda zasu ci gajiyar tallafin sai dai su yi hakuri.

Rahotannin sun nuna cewa, baya ga gidaje da gonaki, ambaliyar ruwa a daminar data gabata ta lalata dinbin hanyoyin mota, gadoji da gine-ginen gwamnati da na cibiyoyi masu zaman kansu a sassa daban-daban na tarayyar Najeriya.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Wasu Mutane Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa a Kano Suka Koka, Martanin Hukuma.mp3