Wasu ayarin ‘yan kasuwa ne da aikin rusau na gwamnatin Kanon ya shafa su ka tunkari Babbar Kotun Tarayya ta Kano don korafi game da lamarin.
Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ne ya bada umarnin rusa dukkanin gine ginen kantuna da shagunan ‘yan kasuwa da ke kewaye da Filin Idin na Kano, ya na mai cewa, gwamnatin da ta shude ta amince da ginen ginen ne ba bisa ka’ida ba, kuma hasali ma an sayar wa ‘yan kasuwar wuraren ne ta haramtacciyar hanya.
Sai dai a hukuncin babbar kotun tarayyar ta nan Kano a jiya Juma’a, karkashin jagorancin Samuel Amobeda ta umarci gwamnatin ta Kano ta biya ‘yan kasuwar diyyar naira miliyan dubu talatin saboda lalata musu dukiya, ba tare da bin dokokin kasa ba.
Mai Shari'a Justice Samuel Amobeda ya ce matakin na gwamnatin Kano cin zarafi ne ga ‘yancin ‘yan kasuwar na mallakar kadara da kuma gudanar da hada hadar kasuwanci wadda kudin tsarin Mulki na kasa ya ba su.
Sai dai gwamnatin ta mayar da martani akan wannan hukunci na babbar kotun tarayya. Barr HARUNA Isa Dederi shi ne kwamishinan shari’a kuma babban Atoni na Kano. “Tun lokacin da aka gabatar da batun a gaban kotun munyi hanzari, munce ba ta da hurumin sauraron karar kuma sigar da aka bi aka gabatar da karar ba siga ce da doka da shari’a suka amince da ita ba, don haka za su daukaka kara kuma muna da kyakkyawan fatan cewa, kotun daukaka kara za ta yi duba na tsanaki akan hujjojin da za mu gabatar mata”.
A cewar sa, hujjoji da shaidun da kotun tayi amfani da su raunana, a don haka bai kamata ayi la’akari da su ba.
Baya ga gwamnatin Kano ‘yan kasuwar na Filin Idi sun gurfanar da hukumar ‘yan sandan Najeriya da hukumar tsaro ta Civil Defence saboda an gudanar da aikin rusau din ne bisa kariya da rakiyar Jami’an su.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5