Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NNPP Ta Maida Martani Game Da Dakatar Da Kwankwaso Daga Jam’iyyar


Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Rikicin cikin gida na Jam’iyyar NNPP na ci gaba da zafafa bayan da uwar Jam’iyyar ta bayyana korar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, mutumin da ya yi mata takarar shugabancin Najeriya a zaben da ya gabata.

Tun a makon jiya ne kwamitin amintattu na Jam’iyyar ya sanar da cewa, ya dakatar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tsawon watanni shida bisa zargin cin amanar Jam’iyyar a zaben daya gabata.

Kazalika, a litinin din nan, Jam’iyyar ta NNPP ta sanar da korar tsohon gwamnan na Kano saboda a cewarta, ya gaza bayyana a gaban kwamitin ladaftarwa domin kare kansa daga tuhumar badakalar wasu kudade kusan naira miliyan dubu guda.

Sai dai Alhaji Hashimu Dugurawa dake zaman shugaban riko na reshen jihar Kano na Jam’iyyar yace tuni kwamitin koli na Jam’iyyar ya kori wadanda ke cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya yi ba dai-dai ba. Ya bayyana cewa, "Wadanda duk suka yi wancan taro na Lagos suna cikin wadanda aka zartar da hukuncin kora daga Jam’iyya saboda dama an same su da laifin cin amanar Jam’iyya a lokutan zabuka, kuma hakan ce ta sanya taron koli na Jam’iyya ya amince cewa a kore su”.

Koda yake wannan batu ne na ciki, amma barakar ta baiwa ‘yan hamayya na waje damar fadin albarkacin bakin su.

Sai dai a jiya talata, jaridun Najeriya sun wallafa rahotan odar kotu dake hana korar Rabiu Musa Kwankwaso daga Jam’iyyar ta NNPP, kuma a cewar Farfesa Kamilu Sani Fage na Jami’ar Bayero Kano hakan na alamta cewa, dambarwa ka iya tsawaita.

Wannan batu na tsallakawa wata Jam’iyya yana cikin batutuwan da Sashen Hausa ya tabo a wata hira da tsohon gwamnan na Kano a kwanakin baya kafin Shugaba Tinubu ya kafa Majalisar Ministoci inda ya bayyana cewa,

“Muna tattaunawa kuma ba’a kammala tattaunawa ba, nan gaba kadan za mu ci gaba da tattaunawa kuma abin da muka ga shawara tayi ko zan shiga wurin su ai ka ga ni ba ni da matsala”.

Wannan dambarwa na zuwa ne a dai-dai lokacin da al’umar jihar Kano ke dakon sakamakon hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe, inda Jam’iyyar APC ke kalubalantar nasarar Jam’iyyar NNPP a kujerar gwamnan na Kano.

Saurari cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG