Kananan Yara A Afrika Na Rashin Abinci Dalilin Sauyin Yanayi

Yara a Afrika

Miliyoyin mutane a kudanci da gabashin Afrika na fuskantar karancin abinci da sauyin yanayi ya haddasa, wanda rabinsu yara ne, a cewar kungiyar bada agaji ta Save the Children.

Yankunan sun fuskanci guguwa mai karfi, da ambaliyar ruwa da kuma fari a cikin ‘yan watannin da suka gabata, yayinda masana kimiya suka ce dumamar yanayi da aka samu da sauri yafi na sauran bangarori na duniya.

Mahaukaciyar guguwar da aka yiwa lakabi da Idai da tayi kaca-kaca da kasar Mozambique a watan Maris, ta kashe mutane sama da dubu 1,300. Guguwar dake tafe da ruwa mai karfi ta shafe Kauyuka da dama, ta kuma cika birane da ruwa makil, yayin da manoma suna gani amfanin gonarsu da dabbobin suna salwanta.

Mahaukaciyar guguwar tana daya daga cikin mafi girma a tarihi, da aka yi kiyasin cewa, ta janyo hasara ta sama da dalar Amurka biliyan biyu ($2B) a fadin yankin.