Kananan Hukumomin Bakassi Da Akphabuyo Basa Hannun Tsagerun Niger Delta

Tsagerun Niger Delta

Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi watsi da rahotannin dake nuna cewa tsagerun Niger Delta na Bakassi Strike Force ne ke rike da ikon wasu kananan hukumomi biyu a jihar Cross River.

Jaridar This Day dake fitowa kullum a Najeriya tace yanzu haka kananan hukumomi biyu Bakassi da Akpabuyo dake jihar Cross River na karkashin ikon tsagerun Niger Delta, jaridar ta kara da cewa tsagerun ne ke tafiyar da al’amuran mulki, inda tace shugabannin kananan hukumomin biyu da kansilolinsu baki daya tuni sun tsere zuwa Calabar fadar gwamnatin jihar.

Wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina, ya tuntubi hedkwatar tsaron Najeriya kan ko me zata ce kan hakan, Janaral Rabe Abubakar shine kakakin hedkwatar wanda ya tabbatar da cewa wannan labari maganace wadda bata da tushe, haka kuma sojoji na can suna kula da tabbatar da cewa akwai kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Duk dai da rundunar sojan kasar na musunta wannan magana amma abune sananne cewar jihar Cross River na fama da aika aikar ‘yan tsageru, inda ko a ‘yan kwanakinnan ma sai da gwamnan jihar Farfesa Benedict Ayade, ya roki shugaban kasa da ya fadada sintirin soji na Operation Delta Safe ya zuwa jihar ta sa.

Saurari cikakken rahotan.

Your browser doesn’t support HTML5

Kananan Hukumomin Bakassi Da Akphabuyo Basa Hannun Tsagerun Niger Delta - 2'16"