Najeriya na daya daga cikin Kasashen da ake biyan haraji mafi kankanta a kan taba sigari, wanda hakan ke karfafa gwiwar mutane musamman mata da matasa har ma da masu karancin shekaru ta’ammali da shi. Kuma cikin rahoton bincike da kugiyar CISLAS tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyin masu sa ido a tsarin biyan haraji a Afirka suka yi , an gano cewa akwai kamfanonin dake sana’ar taba sigari da ke kauce wa biyan haraji kana ana amfani da su wajen wawure kudaden kasa. Awwal Musa Rafsanjani, shugaban kungiyar CISLAC a Najeriya, ya ce:
‘’Mun ga yadda suke ba wasu shugabanin kasashen Afirka cin hanci don su tsira da kudaden da ya dace ace sun biya haraji da zai taimaka wa kasa, sama da dala biliyan 88.6 Afirka ke asara akan gujewa ko kuma sace kudaden da wadannan kamfanoni ke yi, su na da kudade masu tarin yawa baya ga sanya yaranmu ta’ammali da tabar sigari da wiwi dake illata jikinsu ‘’
Masanin tattalin arziki a Najeriya Dakta isa Abdullahi ya kwatanta yadda ake mutunta biyan kudaden haraji a kasashen da suka cigaba don ciyar da al’ummarsu gaba, sabanin wasu kasashen Afirka dake yi wa hakan rikon sakkainar kashi.
Ana ganin rahoton zai taimaka wa kasashen Afirka gyara tsarin harajin da ya dace da kuma takaita yanayin yadda ake ta’ammali da taba sigari da zukar hayakin tabar shisha da ya zama ruwan dare a wasu kasashen Afirka,
Shugaban tsare tsare na kugiyar vision for Alternative development dake kasar Ghana Labaran Musa Mas’ud ya bukaci sauran gwamantocin kasashen Afirka da su haramta ta’ammali da tabar shisha a kasashensu la’akari da dimbin illar da take da shi ga lafiyar dan adam
Rahotani sun yi nuni da cewa a duk shekara ana asarar rayukan mutane miliyan takwas a duniya, sakamakon cututtukan dake da alaka da Shan taba da zukar hayakin shisha, don haka aka bukaci gwamnati ta sa ido a wadannan kamfanoni dan tabbatar da biyan haraji.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim
Your browser doesn’t support HTML5