Kamfanonin China Na Kokarin Maye Gurbin Na Faransa Dake Barin Iran

Shugaban Iran Hassan Rouhani

Gabanin takunkumin da Amurka za ta kakabawa Iran, kamfanonin Faransa na ficewa daga kasar ta Iran yayinda na China kuma ke kokarin maye gurbinsu

Ga dukkan alamu, China na shirin maye gurbin kamfanonin Faransa masu kera motoci, wadanda suka dakatar da aikace-aikacensu a Iran gabanin shirin Amurka na sake maido da takunkumin karya tattalin arziki akan kasar ta Farisa.

Akwai kuma yiwuwar, wannan mataki da Chinan ke so ta dauka, ya sake haifar da wata ‘yar-tsama tsakanin hukumomin Washington da Beijing, matakin da zai sake dagula takaddamar cinikayya da kasashen biyu ke ta hura hanci akai.

Kamfanin kera motocin Renault na Faransa, wanda kashi 8 cikin 100 na motocin dake Iran shi ya kera su, inda Iran din ce ta 12 a girman kasuwar sayen motoci a duniya, ya bayyana a watan da ya gabata cewa, zai bi sahun kamfanonin sama da 100 da suka janye daga Iran, gabanin takunkumin Amurka da ya fara aiki a ranar Talata, duk da cewa kamfanin na Renault ba ya kera mota a Amurkan.

Kamfanin Peugeot ya bayyana shirinsa na ficewa daga Iran a watan Yuni, kamfanin da ke samun kashi 34 cikin 100 na cinikin mota da ake yi a kasar, inda ya kan sayar da motoci dubu 500 a duk shekara.