Lokacin bukuwan watannin Nuwamba da Disamba kamfanonin Amurka zasu yi ciniki sosai fiye da tsammani.
WASHINGTON, DC —
Sabbin alkaluma da aka bayyana sun nuna cewa ‘yan kasuwar Amurka zasu kwashi garabasa lokacin hadahadar da ake yi a duk karshen shekara.
Galibin kantunan Amurka suna ganin karin ciniki a watannin Nuwamba da Disemba, a dai dai lokacinda jama’a suke tunkarar bukukuwan addini dana girmama kasarsu, da suka bukaci bada kyaututtuka da hidimomin iyali. Yawan ciniki da kanti zai yi shine zai banbanta yawan riba ko faduwar da zai yi.
Wani sabon kididdigar da wani kamfani da ake kira Accenture ya gudanar ya nuna jama’a suna da kwarin guiwa gameda samunsu da kuma tabbacin dorewar aiki da suke yi, saboda haka basu da damuwar wajen kashe karin kudade a lokacin hutu ko bukukuwan.