Kamfanoni Aika Sakwanni Kudade Sun Koka Kan Yawaitar Aiyukan 'Yan Fashi A Nijer

Yan fashi

A jamhuriyar Nijer kamfanonin cikin gida masu hada hadar aika sakwannin kudade sun bayyana damuwa dangane da yadda ‘yan fashi da makami suka fara yawaita kai hare hare akan ma’aikatansu a sassan kasar.

Ciki kuwa har da Birnin Yamai inda a jiya ma wani dan fashi ya afakawa wata ma’aikaciya koda yake dubunsa ta cika.

A hirarsa da Muryar Amurka, shugaban kamfanin Al’izza Transfert Alhaji Mohamed Bakay ya yi kiran hukumomi su dubi wannan lamari da idon rahama.

Alhaji Mohamed Bakay ya ce wannan al'amari ya fara yawa kuma yana wakana a wuraren da ba a zato. Abubuwa da dama irin na ban mamaki ne ke faruwa a yau wadanda suka saba da al'adunmu kuma abu ne da za a yi alkantawa da dabi'ar shaye shaye.

Ya kara da cewa suna fatan Allah ya yi maganin matsalar sannan gwamnatin Nijer ya kamata ta dubi abin da idon basira.

Yawaitar kai wa gidajen aika sakwannin kudade matsala ce dake barazana ga rayukan ma'aikata sannan abin na iya shafar harakokin wadanan kamfanoni dake bada gudunmowa wajen bunkasa tattalin arziki. Aikin tsaro aiki ne da ya rataya a wuyan gwamnati.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

KORAFIN KAMFANONIN AIKA SAKON KUDADE.MP3