An kammala samun gwajin lasisin na fasahar akan kudi dalar Amurka miliyan 273.6 daga ko wannensu karkashin hukumar sadarwa ta Najeriya NCC.
Wannan nasarar na zuwa ne bayan amincewar gwamnatin kasar bisa ingancin amfani da fasahar 5G bayan gwaje-gwaje da shawarwari da aka yi a cewar Minister Sadarwa Ali Isa Pantami.
Lasisin da aka bayar dai guda biyu ne kuma kamfanoni sadarwa uku ne wato MTN, Airtel da Mafab wanda suka tsalake zuwa takarar cancanta shiga neman lasisin, amma daga karshen biyu daga ciki su ka yi nasara a cewar Farfesa Umar Garba Danbatta shugaban hukumar ta NCC.
Shi kuma Shugaban kamfanin Sadarwa ta Mafab Dakta Musbahu Mohammad Bashir ya yi karo da cewa ‘yan Najeriya za su ci moriyar wannan lasisin da suka samu.
Aliyu Saidu Abubakar kwamishana dake wakiltar Arewa maso gabashin Najeriya a hukumar ta NCC ya bayyana cewa akwai alfanu mai tarin yawa da wannan sabuwar fasaha ta zamani zata yi wa al’ummar Najeriya mussaman yankin Arewa dake fama da matsalar tsaro.
Ana sa ran wannan sabuwar fasahar ta 5G za ta soma aiki a Najeriya daga sabuwar shekara ta 2022 mai kamawa.
Sauari rahoto cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim:
Your browser doesn’t support HTML5