WASHINGTON, D.C. —
Katafaren kamfanin Qualcomm ya bada sanarwar kamfanin wayar hannu na kasar China mai suna Huawei na gab da kaddamar da sabuwar wayar sa mai suna Mate 20, wadda aka kayata kuma take dauke da nau’ukan Galaxy10.
Ana kyautata zaton cewa wannan waya zata yi gogaiya da manyan wayoyi na zamani musamman a wajan inganci da kuma sauran wasu abubuwa kamar su karfin batiri, sararin ajiya da kuma kyakkyawar kyammarar daukar hoto.
Ku Duba Wannan Ma A Karo Na 2 Facebook Ya Dakile Manhajar Tambaya A Shafin ShiA wani taron manema labarai da Kamfanin ya gudanar, bai fito ya bada wani cikakken bayani akan ranar da Huawei zai fitar da wayar ba haka zalika kudin ta, amma ya yana so duniya ta san cewa ya dauki aniyar ba kwastomomin sa dama domin cin moriyar amfani da wayar mai 7nm Chips, wannan sabuwar fasahar sadarwa ta zamani.