Kamfanin Sadarwa na Twitter ya mayar da martani kan matakin da Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya dauka na dage takunkunmin dakatar da aiki da aka kakaba wa kamfanin watnani 4 da suka wuce.
Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed ya ce Twitter ya amince da sharuddan da aka gindaya masa, wani abu da masana tattalin arziki suka ce babbar nasara ce ga kasar.
A wani taron manema labarai a babban birnin tarayya Abuja, Ministan yada Labaran Najeriya Lai Mohammed ya ce kamfanin Twitter na ci gaba da tattaunawa da Gwamnatin Najeriya kuma sun himmatu wajen tsara hanyar ci gaba domin a maido da aikin kamfanin nan ba da jimawa ba.
Lai Mohammed ya ce ya samu sako daga shugabanin kamfanin inda suka amince da matakan, tare da da bin umurnin mahukuntan kasar.
Lai ya ce kamfanin zai dauki wasu matakai wadanda suka hada da mutunta ikon Najeriya, da kula da muhimman abubuwa da suka ji6anci tsaron kasar da hadin kan ta kafin a maido ta shi.
Ministan ya ce dole kamfanin ya yi rajista a Najeriya, tare da bude Ofis a kasar, sannan a na ta bangaren, Najeriya za ta tabbatar da cewa kamfanin ya samu damar yin aiki don inganta rayuwar ‘yan kasa da ke amfani da dandalin musamman ta hanyar kasuwanci.
Masanin tattalin arziki Abubakar Ali ya yi nazari akan batun inda ya ce wannan mataki babban nasara ce ga Najeriya, domin in Kamfanin ya bi sharuddan da aka gindaya masa, tattalin arizikin kasar zai bunkasa kuma matasa da dama za su samu ayyukan yi.
Abubakar ya ce kamfanin zai zage damtse wajen hana a yi wa kasa ta'annati ko zagon kasa wajen amfani da dandalinsa.
Shi ma wani kwararre kuma masanin harkokin sadarwa mai amfani da dandalin Twitter Auwalu Abdullahi ya ce ya yaba da wanan abu da ya faru tsakanin Najeriya da Kamfanin Twitter domin yana ganin nasara ce aka samu.
A ranar 5 ga watan Yuni na wannan shekara ne Gwamnatin Tarayya ta dakatad da kamfanin Twitter bayan da kafar sada zumuntar ta goge wani sako da Shugaba Mohammadu Buhari ya wallafa a dandalin ta domin a cewarsa ya saba ka’idarsa.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5