Kamfanin Shell Yana Shirin Sake Farfado Da Muhallan Ogoniland

Wan nan mai ne kan ruwa a wani tabki dake a yankin Ogoniland.

Kamfanin mai Shell yace ya dauka da muhimancin gaske rahoton MDD dake nuna yadda yoyon mai ya yi matukar gurbata Ogoniland dake yankin Niger Delta a Najeriya.

Kamfanin mai Shell yace ya dauka da muhimancin gaske rahoton MDD dake nuna yadda yoyon mai ya yi matukar gurbata Ogoniland dake yankin Niger Delta a Najeriya

Darekatan kamfanin a Najeriya Mutiu Sunmonu ya gayawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa Shell zai yi nazarin rahoton sosai da nufin duba hanyoyin sake farfado da muhallin yankin ya koma yadda yake ada cikin hanzari. Yace yoyon mai ba ga mutane da muhalli kadai yake illa ba, har ma ga kasuwanci.

Rahoton da reshen kula da muhalli na MDD ya bayar cikin makon jiya ya bayyana dalla dalla tsananin yadda yoyon mai ya gurbata muhallli da kuma barazana ga lafiyar jama’a a yankin Ogoniland.

Rahoton yace sakamakon aikin hakar mai a cikin shekaru hamsin da suka wuce ya haddasa gurbacewar muhalli da ruwa cikin karkashin kasa fiye da yadda ake zato.Rahoton yace aikin sake tsabtace yankin zai kasance aiki irinsa mafi girma da aka taba yi. Kuma rahoton yace Shell ya gaza wajen kiyayewa da kula da rijiyoyin hakar mansa dake yankin Ogoniland.

Darektan kamfanin a Najeriya Sunmonu ya aza kashi 70% cikin dari na yoyon mai a yankin Niger Delta kan ‘yan zagon kasa da kuma tsageranci.