Nigeria ta iza keyar wani dan kasar zuwa nan Amirka, saboda ana zarginsa da laifin yana da hannu dumu dumu a cikin wani shirin damfara da suka damfari wasu kamfanonin lauyoyin nan Amirka fiye dad ala iliyan talatin.
Jiya juma’a jami’an igeria suka ce shi wannan mutumin mai suna Emmanuel Ekhafor, wanda sdan Nigeria ne an danka shi hannun jami’an Amirka a farkon mako, aka kuma caje shi a jihar Pennslyvania dake gabashin Amirka.
Sun baiyana cewa Emmanuel yana da hannu cikin wani shirin damfara daya danganci mutane da dama. Jami’ai sun baiyana cewa, wannan shirin zamba cikin amince ya kan danganci wani mutum da zaiyi karya cewa yana da matsala dangane da bashi da ake binsa, inda zai nemi wani kamfani lauyoyi domin a taimaka masa. Daga nan wani dan damfarar, shi kuma sai yace zai biya kudin da ake bin mutumin ta hanyar amfani da chek na bogi. Kamfanin lauyoyi sai suka buga wa banki waya domin tabbatar da cewa akwai wannan kudi, to dama da yake a shirye su, sai wani dan danfarar , shi kuma sai yayi karyar cewa shi ma’aikacin bankin ne , ya bada amincewar cewa akwai kudin.
Ta hanyar amfani da wannan dabarar, su wadannan yan 419 sai su karbi kudi daga kamfanin lauyoyin, kafin kamfani ko kuma kamfanonin sun nnkara cewa ceki din da aka basu na bogi ne.
Jami’an Nigeria sunce kamfanonin lauyoyi da lauyoyi tamanin aka yiwa wannan damfara.