Kamfanin mai na shell mallakar Royal Dutch ya yi tayin sayen kamfanin makamashi Cove, dake da hannayen jari a kasashe dabam dabam na gabashin Afrika.
Kamfanin Shell ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya bayar yau Laraba cewa, ya yi tayin sayen kamfanin Cove kan kudi dala biliyan daya da miliyan dubu dari biyar, yayinda a nashi bangaren, kamfanin Cove yace hukumar darektocinshi zata sanar da masu hannayen jari a kamfanin.
Kamfanin Cove yana da hannayen jari a ayyukan hakar mai da iskar gas a kasashen Mozambique da Tanzania da kuma Kenya.
Biyu daga cikin lasisin kamfanin na gonakin iskar gas ne da aka samu bara a gabar tekun kasar Mozambique.
Kamfanin Shell yace tayin da yayi ya ta’alaka kan samun amincewa a rubuce daga ministar albarkatun mu’adina na kasar Mozambique, Esperanca Bias.