Kamfanin Rosetta Stone Ya Kaddamar Da Na'ura Domin Koyon Yaruka Daban Daban

Wani shahararren kamfani mai suna Rosetta Stone dake samar da n'urar koyakaratu a duniya ya kadammar da wata na'ura da zata iya koyawa kananan yara koyon karatu da rubutu da kuma fahimtar wani harshe da ba nasu ba.

Kamfanin ya hada gwiwa ne da wasu kwararru a fannin karatu da rubuce rubuce wadanda ake kira literacy specialist ne suka kirkiro wata dabara da ake kira Laxia learning a turance, kuma shirin na ba yara 'yan shekara uku zuwa bakwai damar koyon karatu da kansu.

Sjirin zai taimaka masu domin samin ilimin na'ura mai kwakwalwa wanda zai fadada fahimtar su da sauri domin cimma burin su na ilimin zamani.

Shugaban kamfanin Rosetta Stone yace idan yara suka koyi karatu da wuri nada damar kammala karartu ba tare da wata matsala ba, ya kara da cewa wannan na'ura na taimakama miliyoyin yara koyon karatu da kuma fahimtar wasu harsuna daban baya ga nasu.