Ginin Taipei 101, na kasar Taiwan, yana da hawa 101, yana daga cikin wadanda sukafi tsada a duniya, an kammala ginin shi a shekarar 2004, an kiyasta kudin ginin da ya kai dallar Amurka billiyan $1.8B. Kana ginin The Palazzo, a garin Las Vegas ta Amurka, wanda yake Otel, da yafi kowane otel tsada a garin an kamala ginin a shekarar 2007, an kiyasta kudin ginin da ya kai dallar Amurka billiyan $1.9B.
Burj Khalifa, na kasar Dubai, yana daga cikin ginanuwa da suka ci kudi wajen gina su, gini ya zama gini na farko da mutun ya taba ginawa a doron kasa da yafi tsawo. An kiyasta kudin ginin da ya kai dallar Amurka billiyan $1.5B. yana da tsawon mita 829. Ginin Sheraton Huzhou Hotel, a kasar China, yana daga cikin ginanuwa da sukafi ban sha’awa a duniya, don kuwa yana kama da kwallo, an kiyasta kudin ginin da ya kai dallar Amurka billiyan $1.5B.
Kyoto Station, na kasar Japan, shine na biyu da yafi girma a kasar, wannan tashar jirgin kasan ba kawai wajen shiga jirgin bane, harma da kasuwa da wajen shakatawa da kalle kalle, an kiyasta kudin ginin da ya kai dallar Amurka billiyan $1.25B. Na gaba kuwa shine Capitagreen, a kasar Singapore, shine ginin da yafi kowannen sabunta, an kamala gini a shekara 2014, an kiyasta kudin ginin da ya kai dallar Amurka billiyan $1.4B. Ginin Royal Adelaide Hospital, na kasar Australia, shima dai ana kan aikin shi wanda ake sa ran idan aka kammala shi zai kai kimanin billiyan $2.1B.