Kamfanin na Arik dai zai koma aiki ne a birin na Maiduguri daga ranar litinin 10 ga watan Mayun nan da muke ciki.
Kamfanin ya ce fasinjoji da ke tashi daga jihar Legas za su iya ci gaba da tafiyar su daga birnin Abuja.
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai kamfanin na Arik, Kyaftin Roy Ilegbodu, ya fitar da sanyin safiyar yau talata inda yeke cewa, suna murna matuka da sake dawowa da aikin jigilar fasinjoji daga Maiduguri sakamakon yadda fasinjojin kamfanin suka dade suna bukatar komawa zirga-zirgan kamfanin a Maiduguri.
Sanarwar ta kara da cewa kamfanin Arik zai rika zirga-zirga sau hudu a mako a ranakun Litinin, Laraba, Juma’ah da kuma Lahadi tare da tabbatar wa fasinjojin cewa za'a tabbatar da tsaron rayukansu, lafiyarsu da walwala a dukkan mataki na zirga-zirgar.
Haka kuma ta ce ma’aikatan kamfanin a shirye suke su bai wa fasinjojinsu duk kulawar da zasu bukata a yayin tafiyar ta su.
Wannan ba shi ne karon farko da kamafanin na Arik ke dakatarwa da kuma dawowa da aikin jigilar fasinjoji daga Maiduguri ba bayan dakatar da ayyuka na tsawon lokaci.
Idan dai ana iya tunawa, ko a shekarar 2017 ma, bayan shafe shekaru hudu da dakatar da aikin jigilar fasinjoji zuwa Maiduguri, kamfanin na Arik ya koma aiki daga ranar 9 ga watan Mayun shekarar ta 2017.