Kamfanin Intel Ya Kaddamar Da Shirin Da Zai Taimaki 'Yan Matan Najeriya

FILE - Intel Corporation.

A wani kokari na bunkasa harkar ilimin mata a Najeriya, babban kamfanin fasahar nan Intel Corporation ya kaddamar da sabon shiri a radiyo da kuma yin amfani da shafin yanar gizo na Bella Naija.

Shirye shiryen dai na nunin yadda kamfanin Intel ya hakikance wajen ganin yayi duk abin da zai iya don ganin ya taimakawa mata wajen samun ilimi da horo, wanda ya hada da ilimin fasaha.

Shirin radiyon zai mayar da hankali kan duk batutuwan da suka shafi mata musamman ma matasa, inda ake sa ran zai janyo hankalin Miliyoyin ‘yan mata domin samun hanyar kawar da jahilci da kaso 50 cikin 100 na mata.

A shafin yanar gizo kuwa Intel zai yi amfani da fitatcen shafin nan mai suna Bella Naija, domin karfafawa mata da yara gwiwa don tabbatar da ganin maza basu barsu baya ba a fannin ilimin kimiyya da fasaha, har ma da fannin kirkirar kayan fasaha.