A cikin gwaje-gwaje da kamfanin google yake yi, na samar da motoci masu tuka kansu batare da wani ya taimaka musu ba. Kamfanin sun bayyanar da rahoton sun a farko da ya bayyanar da cewar motocin suna kara samun karbuwa da kuma taimakawa wajen rage haddura a kan tituna.
Rahoton nasu ya bayyanar da irin bukatar da ake da na samar da wata hanya da motocin zasu dinga, yin oda wato hon ga sauran matuka wasu ababen hawa da mutane. Sun ce yanzu kokarin su shine, ya zamana mototcin suna yin hon din ta yadda baza su rudar da wanda suke yima hon din ba.
Kokarin su shine, ya zamana a wannan matakin sun ganar da motar yadda da kuma a inda ya kamata suyi hon, don samun gyaran hanya da kauce ma hadari. Suna kara kaimi, wajen ganin motocin su, sun aiwatar da aikin su yadda ya kamata, batare da batama matuka sauran abun hawa rai ba.