Huawei kamfanin dake kera wayoyin zamani ya doke kamfanin Apple inda ya zama kamfani na biyu a duniya wajen sayar da wayoyin zamani.
Hakan yasa a karo na farko tun lokacin da Blackberry da Nokia suka mamaye kasuwar waya, Apple ya koma na uku a jerin kamfanonin waya da suka fi ciniki a duniya.
A wani bincike da aka gudanar an gano cewa Huawei ya wuce takwaransa Apple a kasuwar sayar da hannun jari a watan Yuni da Yuli, sai dai ana ganin haka ba zai dawwama ba ganin yadda Apple zai bayyana sabuwar wayar iphone cikin mako mai zuwa.
Shekaru biyar da suka gabata dai kamfanonin Samsung da Apple ne suka mamaye kasuwar kasuwar waya a duniya, sai gashi Huawei ya shiga tsakani.
Tun shekarar 2010 Apple ya zamanto ‘daya daga cikin kamfanoni biyu da suka mayaye kasuwar waya, lokacin da ya wuce BlackBerry kafin ya dane gurbin kamfanin Nokia.
Duk da yake dai kamfanin Huawei ya dade da kafuwa a duniya, amma baiyi fice ba a kasasehen yammacin duniya sai a ‘yan shekarun nan, yayi ta kokarin yin gwagwarmaya da Apple da Samsung a fannin sayar da wayoyi masu tsada, amma wayoyin kamfanin masu rahusa sunyi fice a kasar China da kasashen kudancin Amurka da kuma gabas ta tsakiya da Afirka.
Your browser doesn’t support HTML5