Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tanzania Zata Kaddamar Da Jirgin Sama Mara Matuki Mafi Girma A Duniya Domin Daukin Gaggawa


A Tanzania an shirya kaddamar da jirgin drone mai tuka kansa mafi girma a duniya cikin watan Janairu mai zuwa, domin ‘daukar magani da jini a asibitoci don ceto rayuka.

Shi dai wannan jirgin drone da aka kera shi a jihar California an tsara zai rika kai magunguna har 2,000 zuwa sama da cibiyoyin kula da lafiya 1,000 a rana, cikin kayayyaki da zai kai har da jini da alluran rigakafi da maganin wutar cizon sauro da kuma maganin cutar nan mai karya garkuwar jiki.

An shirya wannan aiki ne domin ceto rayukan mutanen da ke bukatar agajin gaggawa, bayan da aka kaddamar da irinsa a kasar Rwanda wanda ya zamanto nasara.

A cewar Lilian Mvule mai shekaru 51, ta ce wannan abu da za a fara yayi dai dai, bayan da ta tuna yadda ta rasa jikarta a dalilin cutar cizon sauro shekaru biyu da suka gabata. Wadda ke bukatar karin jini cikin gaggawa amma babu jinin a asibitin da take.

Cutar cizon sauro ta zama wata babbar kalubale a kasar Tanzania, wanda har ta kai ga yara ‘yan kasa da shekaru biyar suna bukatar karin jini a duk lokacin da suka kamu da cutar. Idan kuma babu irin jinin da suke bukata, yawanci sukan mutu nan take.

Tanzania babbar kasa ce wadda ta fi girman Najeriya, ta kuma ninka Birtaniya har sau hudu, wanda hakan ya sa yake da matukar wahala ga gwamnatin kasar ta iya rarraba duk magunguna da kayan aikin da ake bukata na gaggawa a duk asibitocin kasar.

Su dai irin wadannan jiragen drones su kanyi tafiyar kilomita 100 cikin a awa, wanda yake ba za a iya kwatanta shi da tafiyar mota ba. Gwamnatin Tanzania dai na fatan wannan shiri zai taimaka wajen ceto dubban rayuka a fadin kasar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:45 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG