Kamfanin Facebook Zai Fara Sanarda Mutane Miliyan 87 Da Aka Yi Anfani da Bayanansu

Shugaban kamfanin Facebook Mark Zukerberg

Yayinda ake sa ran cikin wannan makon ne shugaban kamfanin Facebook Zukerberg, zai bayyana gaban majalisun dokokin Amurka, kamfanin ya sanar cewa zai fara sanarda mutane fiye da miliyan 87 da aka yi anfani da bayanansu ba tare da saninsu ba.

A dai dai lokacinda mai kampanin Facebook Mark Zuckerberg a makon nan yake shirin bada bahasi a gaban majalisun dokokin Amurka a kan ayyukan kampaninsa, inda Amurkawa suka farga kan yawan bayanan da irin wadannan kampanonin fasahar suka tattara gameda da su.


Kampanin Facebook yace zai fara sanar da mutane miliyon 87 a cikin wannan mako, da aka bada bayanansu ga kamfanin dake baiwa 'yan siyasa shawara watau Cambridge Analytica ba da tareda saninsu ba. Facebook ya kuma fara wasu sauye sauye ta yanda masu amfani dashi zasu kiyaye bayanansu cikin sauki.


Duk da cewa wadannan da wasu sauye sauye zasu kara karfafawa masu mu'amala da Facebook gwuiwa gameda tsaron bayanansu, batun yana ci gaba da haska fitila kan tambayar data firgita Amurkawa; wane irin bayanan mutane kampanonin Google da Facebook ke dasu, kuma me suke yi dasu?